IQNA

Fushin yahudawa  sahyoniyawa kan Sweden bayan ta amince a kona Attaura

18:44 - July 15, 2023
Lambar Labari: 3489475
Stockholm (IQNA) Amincewar Sweden da matakin da wani matashi ya dauka na kona wata Attaura a gaban ofishin jakadancin yahudawan sahyoniya ya fusata mahukuntan yahudawan sahyuniya.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na al-Quds al-Arabi cewa, kafofin yada labaran nahiyar turai sun bayar da rahoton cewa, ‘yan sandan kasar Sweden sun samu bukatu da dama na kona littafai masu tsarki a wurare daban-daban a birnin Stockholm.

Jaridar Yedioth Aharonot ta yaren Hebrew ta kuma ruwaito cewa, 'yan sandan Sweden sun amince da matakin da wani mutum ya dauka na kona kwafin Attaura a ranar Asabar.

Matakin da wani matashi dan shekaru 30 da haihuwa ya dauka na kona kwafin Littafi Mai Tsarki da na Attaura a gaban ofishin jakadancin yahudawan sahyoniya da ke Stockholm daga karshe ya fito da muryar mahukuntan sahyoniyawan da suka yi shiru kan kona kur'ani.

Aharonot ya rubuta a ranar Juma'a cewa buga rahotannin da 'yan sandan Sweden suka yi na amincewa da bukatar mutum na kona kwafin Attaura a gaban ofishin jakadancin Tel Aviv da ke Stockholm ya firgita 'yan sahayoniya.

Yayin da take ishara kan laifin kona kur'ani mai tsarki makonni biyu da suka gabata da wani mai tsatsauran ra'ayi ya aikata a gaban babban masallacin birnin Stockholm, wannan jaridar ta ce: Ba a fayyace ainihin wadanda ke neman kona Littafi Mai Tsarki ba; Amma da alama yana so ya kalubalanci yadda Sweden ta bi ka'idar 'yancin fadin albarkacin baki, ka'idar da ta sa Sweden ta amince da kona kur'ani.

Haka nan kuma yayin da take ishara da kokarin da shugabannin musulmi da na Yahudawa suka yi a bayan fage na hana sake maimaita wulakanta litattafai masu tsarki, wannan jaridar ta Ibraniyawa ta ce: Sai dai har yanzu ba a sami sakamako ba.

Aharonot ya nakalto Rabbi Moshe David Hakuhen, wanda ke jagorantar wata majami'a a cikin al'ummomin Scandinavia, yana cewa "Wannan ba lamari ne na adawa da Yahudawa ba ko kuma musamman kan Yahudawa, wannan wani yunkuri ne na kalubalantar 'yancin fadin albarkacin baki da cin zarafinsa saboda laifukan kiyayya."

Wannan malamin ya kara da cewa: "Wannan mutumin yana son ya ga ko gwamnatin Sweden munafuka ce kuma idan sun yarda a kona Littafi Mai Tsarki, kamar yadda suka yarda da kona Kur'ani."

Hakuhen ya kuma ce al'ummar Yahudawa da ke zaune a kasar Sweden na adawa da kona kur'ani da kuma tsayawa kan al'ummar musulmi.

Da yawa daga cikin malaman yahudawan sahyoniya sun fitar da irin wannan sako ga hukumomi da gwamnatin kasar Sweden, inda suka bukaci da kada su bari a kona Attaura.

Shi ma firaministan gwamnatin Sahayoniya Benjamin Netanyahu ya yi Allah wadai da yarjejeniyar da mahukuntan kasar Sweden suka yi na kona Attaura.

Ma'aikatar harkokin wajen gwamnatin Sahayoniyya ta tuntubi ofishin jakadancin Sweden da ke Tel Aviv da kuma hukumomin kasar Sweden inda ta yi gargadi game da hadarin da 'yan sandan kasar Sweden ke da shi na amincewa da wulakanta wurare masu tsarki na Yahudawa.

 

 

 

4155067

 

captcha